Isa ga babban shafi
Myanmar

Myanmar: An gurfanar da Suu Kyi kotu

A yau Laraba aka gurfanar da jagorar Myanmar, Aung San Suu Kyi gaban kotu, kwanaki biyu bayan tsare ta da sojojin da suka kifar da gwamnatin kasar suka yi, a yayin da kiraye kirayen tada kayar baya don nuna adawa da juyin mulkin ke karuwa.

Aung San Suu Kyi.
Aung San Suu Kyi. AFP
Talla

Kasar Myanmar da ke kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta sake fadawa cikin mulkin soji ne bayan da wasu gungun sojoji suka damke jagororin mulkin farar hula, a wasu jerin samame da suka kai a ranar Litinin, lamarin da ya kawo karshen ‘yar gajerar mu’ammala da dimokaradiya da masu kakin suka yi.

Ba sake ganin Suu Kyi a bainar jama’a ba tun da jam’iyyarta ta National League for Demoracy, NLD ta samu gagarumar nasara a zaben watan Nuwamban shekarar da ta gabata, amma sojojin kasar, wadanda jam’iyyarsu ta sha mummunan kaye suka ayyana zaben a matsayin mai cike da magudi.

A wannan Larabar, kakakin jam’iyyar Suu Kyi ta NLD, ta sanar da gurfanar da ‘yar shekara 75 a gaban kotu, a kan abin da ya shafi zargin saba wa dokar fita da shigowa da kayayyaki, amma kotu ta dage sauraron karar har sai nan da makonni biyu.

Wannan tuhuma ta basa bam bam da ake wa jagorar Myanmar din ta samo asali ne daga binciken da aka yi a gidanta biyo bayan kame ta, inda aka gano na’urorin tafe – da – gidanka na walkie-talkies, kamar yadda takardun tuhumar ‘yan sanda da ya shiga hannun manema labarai suka nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.