Dubban 'yan Myanmar sun cigaba da zanga-zangar adawa da sojoji
Dubban ‘yan Myanmar a ranar Lahadi sun cigaba da zanga-zangar adawa da juyin mulkin kifar da gwamnatin Aung San Su Kyii da sojoji suka yi a kasar.
Wallafawa ranar:
Zanga-zangar na cigaba da yin karfi ne duk da matakin katse layukan Intanet dana wayoyin hannu da gwamnatin sojin kasar ta Myanmar ta dauka, wanda rahotanni suka ce ta sassauta shi.
Bayanai sun ce akalla mutane dubu 100 suka fita zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojin na Myanmar a Yangon babban birnin kasar, yayinda wasu dubban suka fantsama kan titunan sauran birane.
Ranar Litinin da ta gabata, malamai da dalibai akalla 200 suka kaddamar da zanga-zangar kin jinin sojojin Myanmar a babbar jami’ar kasar ta Dagon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu