Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mutane 30 sun mutu, 52 sun ji rauni a wata fashewa a Afghanistan

Hukumomin Kasar Afghanistan sun ce akalla mutane 30 suka mutu, yayin da wasu 52 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam kusa da wata makarantar mata dake Yammacin Kabul.

Shugaban Afghanista Afghanistan Ashraf Ghani ya zargi Taliban da kai harin.
Shugaban Afghanista Afghanistan Ashraf Ghani ya zargi Taliban da kai harin. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar Tareq Arian ya tabbatar da adadin sakamakon hadarin da aka samu a yankin Dasht-e-Barchi, unguwar mabiya Shia, lokacin da jama’a suka fita hada hadar sayayyar bikin sallah da ke zuwa a karshen azumin watan Ramadana.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo ta bakin wani da ya tsallake rijiya da baya, Reza yana cewa ya ga mutane da dama jina jina tare da kura da kuma hayaki, yayin da wasu ke kururuwar a taimaka musu.

Reza ya ce ya kuma ga wata mata na bin gawarwakin mutanen da ke kwance tana neman ‘yar ta, kafin daga bisani ta yanke jiki ta fadi bayan ganin jakar ta dauke da jini.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, yayin da kungiyar Taliban ta nesan ta kanta.

Sai dai shugaban kasa Ashraf Ghani ya zargi kungiyar Taliban da kai harin, inda ya ke cewa ba za su yi fada gaba da gaba da jami’an tsaro ba, sai dai kai hari kan fararen hular da basu ji basu gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.