Isa ga babban shafi
Afghanistan

Harin bom ya hallaka mutane 15 tare da jikkata 90 a Afghanistan

Akalla mutane 15 suka mutu yayinda wasu 90 suka jikkata yayin wani harin bom da aka kai da mota birnin Pul-e-Alam na lardin Logar a kudancin Afghanistan yau juma’a. A karon farko bayanai sun bayyana fargabar harin ya hallaka mutane fiye da 30 gabanin tabbatar da adadin daga ma'aikatar Lafiya.

Mutane fiye da 30 ake fargabar sun mutu a farmakin na yau wanda ya rutsa da dalibai.
Mutane fiye da 30 ake fargabar sun mutu a farmakin na yau wanda ya rutsa da dalibai. AP - Rahmat Gul
Talla

Harin wanda ke zuwa dai dai lokacin da dakarun Amurka ke kokarin ficewa daga kasar na diga ayar tambaya kan makomar tsaro a sassan kasar mai fama da hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda kusan shekaru 20.

Mai magana da yawun gwamnan lardin na Logar, Dedar Lawang ya bayyana cewa babu hakikanin alkaluman wadanda suka rasa rayukansu a farmakin kawo yanzu.

Rahotanni sun ce maharan sun sanya bom din ne a cikin wata mota yayinda suka ajje motar gab da wani gidan baki a babban birnin Lardin, gidan da ke dauke da tarin baki da kan shiga yankin musamman dalibai.

Sanarwar da ministan cikin gida na Afghanistan Tariq Arian ya fitar ta nuna cewa zuwa yanzu an gano gawarwakin mutum 15 sai kuma wasu 90 da suka jikkata a farmakin ko da ya ke ya bayyana cewa da yiwuwar alkaluman su karu.

Harin dai ya zo ne kwana guda gabanin dakarun Amurka su fara ficewa daga ta Afghanistan mai fama da rikici, kuma zuwa yanzu babu kungiyar da aka bayyana a matsayin wadda ta dauki alhakin farmakin.

Kungiyoyin Taliban da IS ne ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a sassan kasar ta Afghanistan wajen kai hare hare musamman kan jami'an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.