NATO ta fara janye dakarunta daga Afghanistan
Kungiya tsaro ta NATO ta ce sojojinta, da na Amurka sun fara ficewa daga kasar Afghanistan, kamar yadda shugaba Joe Biden ya bukac i a yi, bayan daukar tsawon shekaru a kasar.
Wallafawa ranar:
Sojojin Amurka da kawayenta sun amince a wannan wata su fara janye sojojin 9.600 daga kasar bayan tsawon lokacin da suka dauka suna yaki a chan kamar yadda wasu jami’an Nato suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa.
An dau watanni ana jan kafa a game da wannan mataki, bayan amincewa da tsohon shugaban kasar Amurika Donald Trump yayi, duk da tsoron kada Talban ta sake kwace iko a kasar.
Sai dai shugaba Biden ya ce sojojin Amurka zasu kammala ficewa daga kasar ne a rana 11-ga watan Satumba da ake cika shekaru 20 Da kaiwa Amurka harin da ya janyo shigar sojinta a Afghanistan.
Ministan tsaron kasar jamus ya bayana cewa sojojinsu 1300 zasu kamala ficewa kasar a watan Yuli.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu