Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Taliban da gwamnatin Afghanistan sun tsagaita wutar kwana 3 saboda Sallah

Mayakan Taliban da Gwamnatin Afghanistan sun yi shelar tsagaita wuta da za ta shafe kwanaki 3 ta na aiki domin bai wa jama’a damar gudanar da bukukuwan sallah karama.

Tawagar wakilcin kungiyar Taliban.
Tawagar wakilcin kungiyar Taliban. © AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

Sanarwar tsagaita wutar da bangarorin biyu suka fitar a yau Litinin, na zuwa sa’o’i bayan harin bam din da ya kashe mutane 11 da ke cikin wata motar bas cikin daren ranar Lahadin nan a lardin Zabul da ke kudu maso gabashin kasar ta Afghanistan.

Ko a ranar Asabar da ta gabata ma sai da wani harin bam din ya kashe mutane akalla 50 tare da jikkata wasu 100 mafi akasarinsu yara 'yammata a kusa da wata makaranta a birnin Kabul yayin da su ke tsaka da sayayyar bukukuwan Sallah.

Sai dai da safiyar yau Litinin kungiyar Taliban ta fitar da sanarwar da ta bai wa mayakanta umarnin dakatar da kai hare-hare har tsawon kwanaki uku domin gudanar da bikin Sallah karama cikin kwanciyar hankali, jim kadan bayan sanarwar kuma shi ma shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya sanar da tsagaita wutar daga bangarensa, inda kuma ya bukaci kungiyar ta Taliban ta amince da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar dindindin don kawo karshen yakin da ke cigaba da tagayyara ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.