Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Taliban ta yi maraba da ficewar dakarun Amurka daga Afghanistan

Illahirin dakarun Amurka da na kungiyar tsaro ta Nato sun kammala janyewa daga sansanin sojin Bagram da ke arewacin birnin Kabul na kasar Afghanistan, matakin da tuni kungiyar Taliban ta yi maraba da shi.

Dakarun Amurka da ke yaki a Afghanistan.
Dakarun Amurka da ke yaki a Afghanistan. REUTERS - STRINGER
Talla

Wani baban jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ya tabbatar da janyewar dakarun baki daya, to sai dai bai bayyana ranar da za a yi bikin mika sansanin ga hukumomin kasar ta Afghanistan ba.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid y ace ficewar dakarun ketaren ne zai baiwa al’ummar Aafghanistan hakikance makomarsu tsakaninsu sabanin shigar da bare cikinsu.

Tsohon shugaban Amurkan Donald Trump ne ya alkawarta ficewar dakarun karkashin tattaunawar kasar da kungiyar ta Taliban da nufin kawo karshen yakin kusan shekaru 20 da Afghanistan ta shafe ta na fuskanta.

Sai dai Kungiyar ta tsananta kaddamar da hare-hare kan dakarun kasar tun bayan fara ficewar dakarun na Amurka, yayinda ta ayyana kwace iko da wasu yankuna lamarin da ke digar ayar tambaya kan ko Afghanistan za ta iya jagorancin yakin ita kadai tare da baiwa al'ummarta cikakken tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.