Isa ga babban shafi
Taliban-IS

Harin IS ya hallaka mayakan Taliban a Afghanistan

Rahotanni daga Afghanistan na cewa mayakan Taliban biyu na daga cikin mutane 3 da suka mutu a wani hari kan shingen bincike da ke lardin Nangarhar a gabashin kasar.

Wasu mayakan Taliban.
Wasu mayakan Taliban. Aamir QURESHI AFP
Talla

Harin na birnin Jalalalbad shi ne na baya-bayan nan da IS ta kaddamar a yankin wanda ke matsayin matattarar mayakan kungiyar kuma inda ta fi cin karenta babu babbaka tsawon shekaru.

Shaidun gani da ido sun ce maharin ya isa shingen binciken ne a cikin babur mai kafa 3 inda ya bude wuta tare da kashe mayakan na Taliban 2 da wani farar hula guda.

Sai dai Taliban da ke tabbatar da farmakin ta ce babu mayakinta ko guda da harin ya rutsa da shi.

Wata majiya ta daban kuma ta tabbatar da yadda mayakan Taliban 2 suka jikkata a kokarinsu na kwance bom din da ake kyautata zaton mayakan na IS ne suka dasa shi.

IS na ci gaba da tsananta hare-hare tun bayan kammala ficewar dakarun Amurka daga kasar inda ko cikin watan Agusta suka hallaka fiye da mutum 100 a wani farmaki da suka kai filin jirgin saman birnin Kabul.

Bangarorin Biyu na Taliban da IS sun samu rarrabuwar kai a al’amuran da suka shafi tafiyar da addini da kuma dabarun yaki duk da yadda kowanne bangare ke ikirarin yaki domin addini, dalilin da ke sanya su fada da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.