Isa ga babban shafi
Taiwan

Gobara ta lakume rayukan mutane sama da 46 a Taiwan

Hukumomin Taiwan suka ce akalla mutane 46 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Alhamis a wani gini dake birnin Kaohsiung, a kudancin kasar.

Gobarar da ta lakume rayukan mutane a wani yankin Kudancin Taiwan, 14/10/21.
Gobarar da ta lakume rayukan mutane a wani yankin Kudancin Taiwan, 14/10/21. AFP - HANDOUT
Talla

Ma’aikatar kwana-kwana a yankin Kaohsiung cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai tace, “Gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 46 yayin da 41 suka samu raunuka.

Gobarar ta tashi ne a wani bene mai hawa 13 dake da gidajen kwana da kantuna da ofisoshi da sanyin safiyar wannan Alhamis, in ji jami'ai, kuma ta lalata benaye da dama kafin jami'an kashe gobara su yi nasarar shawo kan ta.

Hotunan da kamfanin dillancin labarai na Taiwan ya fitar sun nuna hayaki yana tashi daga tagogin ginin yayin da ma'aikatan kashe gobara ke kokarin kashe wutar.

Yawancin wadanda abin ya rutsa da su sun kasance a hawa na bakwai zuwa na goma sha daya, inda gidajen kwana suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.