Isa ga babban shafi
Taiwan-China

Amurka na kintsa dakarun Taiwan don tinkarar barazanar China

Shugabar Taiwan Tsai Ing-wen ya tabbatar  kasancewar wani rukuni na dakarun Amurka a kasar don taimakawa wajen horar da sojojinta, tana mai bayyana yakinin cewa Amurka za ta kare tsibirin a duk lokacin da China ta kai mata hari.

Tsai Ing-wen, shugabar kasar Taiwan.
Tsai Ing-wen, shugabar kasar Taiwan. Handout Taiwan Presidential Office/AFP/File
Talla

A wata ganawa da tashar talabijin ta CNN, Tsai ta bayyana Taiwan a matsayin wata tauraruwar dimokaradiyya a yankin da ke fuskantar kalubale daga makwafciya mai kama karya, a daidai lokacin da barazana da China ke mata ke dada kamari.

Wani jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa da sauran kafafen yada labarai da wannan batu na kasancewar dakarun Amurka a Taiwan.

Wadannan kalamai na shugaba Tsai, su ne na farko daga wani jagoran Taiwan a bainar jama’a, tun bayan da bataliyar sojin Amurka ta karshe ta janye daga tsibirin a shekarar 1979, a lokacin da Washington ta koma huldar diflomasiyya da China.

Kalaman sun janyo kakkausar suka daga China, wadda ta zargi Amurka da kokarin haddasa husuma, tana mai bayyana rashin goyon bayanta ga duk wata hulda ta soji tsakanin Taiwan da Washington.

China na daukar Taiwan, mai cikakkaiyar ‘yancin kai a matsayin wani yanki nata, kuma ta sha alwashin karbo tsibirin ko da karfin tuwo, lamarin da ke ta’azzara zaman tankiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.