Isa ga babban shafi
India

Babban Hafsan Sojin India Janar Rawat ya rasu a hadarin jirgin sama

Ma’aikatar tsaron India tace Babban Hafsan sojin kasar Janar Bipin Rawat na daga cikin mutane 13 da suka mutu a hadarin jirgin saman da aka samu yau laraba.

Wani jirgin yakin India a Kashmir.
Wani jirgin yakin India a Kashmir. AFP/File
Talla

Sanarwar rundunar sojin saman ya ce jirgin da kwamandan ke ciki kirar Mi-17 samfurin Rasha ya yi hadari ne a dai dai Coonoor ta jihar Tamil Nadu.

Rahotanni sun ce Janar Rawat wanda ke rike da mukamin Babban hafsan sojin tun daga shekarar 2019 yana kan hanyar balaguro ne da iyalin shi lokacin hadarin wanda ya ritsa da wau karin mutune 12.

Sanarwar sojin ta bayyana Janar Rawat a matsayin mai yawan tsokaci akan lamuran kasar da kuma zama fitacce a cikin dakarun India da suka sadaukar da rayukan su ga kasar.

Babban hafsan na daga cikin wadanda suka samu raunuka lokacin yakin kan iyakar da India ta gwabza da Pakistan, yayin da ya kuma tsallake rijiya da baya a wani hadarin jirgin sama kafin mutuwar sa a hadarin yau.

Kafin rasuwar Janar Rawat ana kallon sa a matsayin na kusa da Firaminista Narendra Modi, inda lokaci zuwa lokaci ya kan yi tsokaci akan batutuwan da suka shafi manufofin kasashen waje da siyasar yankin Asia da kuma na cikin gida.

A matsayin sa na babban hafsan sojin India, Janar Rawat ya bukaci mutanen India da su dinga jin tsoron dakarun kasar su.

A shekarar 2017, Janar din ya bayyana sojojin India a matsayin masu haba haba da mutane, amma yace lokacin da aka bukace su da su mayar da doka da oda, ya zama dole jama'ar kasa su ji tsoron su.

Marigayin ya fito daga gidan da ake aikin soji tsakanin kaka da kakanni, inda ya zama karamin hafsan soji a shekarar 1978, shekarar da aka harbe shi da bindiga a rikicin Yankin Kashmir.

A shekaru 40 da yayi yana aikin soji, Janar Rawat ya rike mukamai daban daban kafin rasuwar sa ayau sakamakon hadarin jirgin sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.