Isa ga babban shafi

India na kokarin ceto tattalin arzikin ta a wani sabon tsari mai inganci

Indiya ta sanar da shirin bada hayar wasu kadarori mallakar gwamnati ga kamfanoni masu zaman kansu a wani yunkuri na samun kudin shiga da ya kai rupee  tiriliyan 6 (kimanin dala biliyan 81) don farfado da tattalin arzikin kasar da ya shiga wani yanayi saboda annobar korona da kuma samar da sabbin kayayyakin more rayuwa ga jama’arta.

 Narendra Modi Firaministan India
Narendra Modi Firaministan India © AFP - PRAKASH SINGH
Talla

India wacce itace ta uku a karfin tattalin arzikin Asiya ta shiga matsin tattalin arziki saboda tsauraran matakan kulle da ta dauka don yaki da annobar Covid – 19 , lamarin da haifar da gibin kasafin kudi, da kuma shigar da miliyoyin mutane cikin talauci.

Fadar gwamnatyin India
Fadar gwamnatyin India © AFP - SAJJAD HUSSAIN

Karkashin wannan sabon Shirin na gwamnati, Kamfanoni masu zaman kansu za su iya hayar kaddarorin gwamnati na dogon lokaci, kama daga titina masu tsawon kilomita dubu 26, cibiyoyin samar da wutar lantarki, gami da na hasken rana, kafofin sadarwar wayayoyin salula, da kuma kimanin turakun sadarwa kusan dubu 15.

 Narendra Modi Firaministan India
Narendra Modi Firaministan India © AFP - PRAKASH SINGH

Har ila yau, cikin kaddarorin da za’a bada hayarsu ga ‘yan kasuwa har na tsawon 4, sun hada da bututun iskar gas mai tsawon kilomita dubu 8, tashoshin jirgin kasa 15, layin dogo, filayen jirgin sama 25, da filayen wasanni da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.