Isa ga babban shafi
Malaysia

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 14 a Malaysia

Akalla mutane 14 suka mutu yayinda wasu fiye da dubu 70 suka rasa matsugunansu bayan ambaliyar ruwan Malaysia da ke biyo bayan kakkarfan ruwan saman da kasar ta gani a ‘yan kwanakin nan.

Wasu jami'an agaji da ke aikin kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Kuala Lumpur.
Wasu jami'an agaji da ke aikin kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Kuala Lumpur. AP - Vincent Thian
Talla

Rahotanni sun bayyana yadda jiragen soji a kasar ta Malaysia ke ci gaba da aikin raba abinci ga daruruwan mutanen da suka makale a gidajensu wadanda karfin ruwan ya hana jami’an agaji iya kai musu dauki.

Tsawon kwanakin da aka shafe ana ruwan da ya haddasa kakkarfar ambaliyar a karshen mako, ya zama ibtila’I mafi muni da kasar ta gani a baya-bayan nan, bayan da ruwan ya katse wutar lantarki tare da rufe manyan hanyoyin da suka sada birane da kauyuka.

Jihar Selangor mafi arziki a kasar da ke gab da Kuala Lumpur babban birnin Malaysia na jerin yankunan da ambaliyar ta fi yiwa barna.

A birane kamar Shah Alam har zuwa yau talata akwai kakkarfan ruwan da ke hana hada-hada wanda ya tilasta amfani da jiragen saman Soji don kai daukin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.