Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa-Nukiliya

Korea ta Arewa ta sake gwajin wani shu'umin makami mai Linzami

Kasar Koriya ta Arewa ta harba wani abu mai kama da makami mai linzami a cikin teku, abin da kasar Amurka ta yi tir da shi, inda ta bukaci zama a teburin tattaunawa da kasar.

Gwajin makamin da Korea ta Arewa ta yi wanda aka haska yau laraba a gidajen talabijin din kasar.
Gwajin makamin da Korea ta Arewa ta yi wanda aka haska yau laraba a gidajen talabijin din kasar. REUTERS - KIM HONG-JI
Talla

A cikin shekaru 10 da Kim Jong Un ya hau kan karagar mulki, Koriya ta Arewa ta samu ci gaba ba a yi tsammani nan kusa ba, musamman a bangaren fasahar soji, duk da takunkumin da aka kakaba mata.

Kasar da ke da makamin nukiliya ta fara kaddamar da makaman wannan sabuwar shekarar biyo bayan gwajin manyan makamai na shekara guda duk da tsananin matsin tattalin arziki da take fuskanta sakamakon barkewar annobar coronavirus.

Rundunar sojan Koriya ta Kudu ta ce takwararta ta Arewa ta harba wani abin da ake kyautata zaton makami mai linzami ne zuwa gabashin teku  daga lardin Jagang da ke kan iyaka da kasar Sin.

To sa  dai Amurka ta ce wannan kaddamarwar ya saba wa kudirorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda kuma ya kasance babbar barazana ga al’ummomin duniya.

Tuni dai sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sakataren tsaro Lloyd Austin suka shirya ganawa kan harkokin tsaro da takwarorinsu na Japan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.