Isa ga babban shafi
Iraqi

Majalisar dokokin Iraq ta dage zaben shugaban kasa

Majalisar dokokin Iraqi ta dage babban zaben shugaban kasar har sai baba ta gani, bayan da mambobi 58 cikin 329 da suka halarci zaman majalisar suka kada kuri'ar amincewa da dakatar da zaben.

Barham Salih, shugaban Iraqi.
Barham Salih, shugaban Iraqi. AFP/Archivos
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan da kasar ta shafe tsawon watanni 4 tana fama da rikicin siyasa da yaki ci yaki cinyewa, sakamakon babban zaben da bai kammala ba, wanda hakan ya sa ba’a samu sabon Prime minister ba.

To sai dai ana sa ran watakila sauran mambobin majalisar za su yi fatali da dokar, duk da yadda sauran mambobin suka amince da dage zaben mai cike da sarkakiya.

Da yake sanar da dage zaben, daya daga cikin manyan masu zaben sarki, kuma babban jigo a gwamnatin kasar Moqtada Sadr ya ce a yanzu babu halin yin zabe a kasar har sai abubuwa sun daidaita.

A cewarsa, wannan na cikin wani tsari na kare kasar daga fadawa cikin tsananin rikicin bayan zabe, da ka iya biyo baya, matsawar ba’a yi shiri na tsanaki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.