Isa ga babban shafi
Afghanistan

Cutar Kyanda ta kashe sama da mutum 150 cikin wata daya a Afghanistan

Hukumar Lafiya ta Duniya tace Cutar kyanda da ta barke a Afganistan ta kashe mutane 150 cikin wata tare da kama dubun dubatar mutane, tana mai gargadin adadin mace-macen na iya karuwa.

Cutar kyanda na kashe mutane a Afghanistan
Cutar kyanda na kashe mutane a Afghanistan ANP/AFP/File
Talla

Hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce annobar ta fi daukar hankali musamman tun bayan da Afganistan ta fara fuskantar matsalar karancin abinci masamman abinci mai gina jiki, lamarin da ya sa yara ke fuskantar kamuwa da cutar mai saurin yaduwa.

Kakakin hukumar ta WHO Christian Lindmeier ya shaida wa manema labarai a Geneva cewa, "An samu karuwar masu kamuwa da cutar ta kyanda a dukkannin larduna tun daga karshen watan Yulin shekarar 2021."

Lindmerer yace daga watan Janairu, cutar ta kama sama da mutum 35,319, ciki har da 3,000 da aka tabbatar a dakin gwaje-gwajen kimiyya, yayin da 156 suka mutu.

Kashi 91 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar da kuma kashi 97 na wadanda suka mutu yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.