Isa ga babban shafi
Taliban-WHO

WHO na tattaunawa da Taliban kan ayyukan jinkai a Afghanistan

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya gana ministan lafiyar Taliban da ke kasar Faransa dangane da tabarbarewar ayyukan jinkai a kasar Afghanistan.

Wasu wakilan Taliban.
Wasu wakilan Taliban. AP - Stian Lysberg Solum
Talla

Gebreyesus ya ce sun tattauna da Qalender Ebad wanda ke cikin tawagar Taliban da ke ziyara a Geneva domin tattaunawa da hukumomin duniya.

Shugaban hukumar Lafiyar yace duk da dan ci gaban da aka samu a Afghansitan har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da ayyukan jinkai wanda ke jefa rayuwar jama’a cikin kunci.

Gebreyesus yace sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi bunkasa harkokin kula da lafiyar jama’a da ayyukan gagagwa da kuma batun horar da ma’aikata.

Tsedros yace babbar bukatar Afghansitan ayau itace samun kayan gwajin annobar korona, musaman nau’in omicron anin yadda adadin masu fama da cutar ke karuwa a kasar.

Gwamnatin Switzerland ta gayyaci wakilan gwamnatin Taliban domin tattaunawa da su akan halin jinkai da kuma bada ilimi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.