Isa ga babban shafi
China-COVID-19

Mutane 2 sun mutu a China sakamakon harbuwa da COVID-19

A yau Asabar ma’aikatar lafiyar China ta sanar da cewa mutane biyu sun mutu sakamakon harbuwa da cutar Covid -19 a karon farko cikin sama da shekara guda kenan, kuma dukkanninsu daga lardin Jilin.

Shugabann China, Xi Jinping.
Shugabann China, Xi Jinping. AP - Andy Wong
Talla

Wannan na zuwa ne a lokacin da kasar ke fama da sake bayyanar cutar mai tsanani tun bayan bullar annobar a 2019.

Wannan ne karon farko da China ta sanar da asarar rai sakamakon wannan cuta tun bayan ranar 26 ga watan Janairun 2021, lamarin da ya kai adadin wadanda cutar ta lakume a kasar zuwa dubu 4 da dari 6 da 38.

 China ta sanar da sabbin wadanda suka harbu da wannan cuta da adadinsu ya kai dubu 4 da 51 a yau Asabar, kasa da dubu 4 da 365 da aka samu a Juma’a.

A  birnin Wuhan na kasar  ne wannan annoba ta bulla a shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.