Isa ga babban shafi
Sri Lanka

Shugaban Sri Lanka ya yi tayin rarraba mukamai da 'yan adawa

Shugaban kasar Sri Lanka wanda ke fuskantar matsin lamba  ya yi tayin  raba madafun iko da ‘yan adawa a yau Litinin,a yayin da zanga zangar neman ya yi murabus ke ta’azzara sakamakon karancin abinci, makamashi da magunguna da ya addabi kasar.

Gotabaya Rajapaksa shugaban Sri Lanka.
Gotabaya Rajapaksa shugaban Sri Lanka. AFP/File
Talla

Wannan tayin da shugaba Gotabaya Rajapaksa ya mika wa majalisar dokokin kasar na zuwa ne a yayin da jami’an tsaro dauke da makamai suka yi damarar dakile karin zanga zanga a kan abin da gwamnatin da kanta ta bayyana a matsayin karancin mahimman kayayyakin masarufi  da makamashi mafi muni tun bayan da kasar ta samu yanci daga Turawan Birtaniya a shekarar 1948.

A wata sanarwa, shugaba Rajapaksa ya gayyaci dukkannin jam’iyyun siyasa dake majalisar dokokin kasar da su karbi mukaman ministoci da za a ba su, tare da goyon bayan kokarin lalubo mafita ga matsalolin da suka addabi kasar.

Ya jaddada cewa za a samu masalaha ga matsalolin da suka addabi kasar ne kawai ta hanyar dimokaradiyya,  a yayin da dubban mutane ke zanga zanga ta bai-daya a birane, garuruwa da kauyukan kasar.

Dukkannin ministocin kasar sun yi murabus

Wannan matakin na shugaba Rajapaksa na zuwa ne bayan da dukkannin mabobin majalisar zartaswar kasar, banda Rajapaksa da yayansa Firaminista Mahinda Rajapaksa, suka mika takardun murabus dinsu a daren Lahadi.

A waje daya kuma, shi ma gwamnan babban bankin kasar, Ajith Cabraal wanda ya dade da nuna adawa da kudin tallafi daga asusun bada lamuni na duniya IMF ya  sauka daga mukaminsa a Litinin dinnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.