Isa ga babban shafi
Srilanka-Tattalin arziki

Babban bankin Sri Lanka ya kara kudin ruwan da ya ke sawa kan bashi

Babban bankin kasar Sri Lanka da a yanzu haka ke fama da karancin kudi ya kara yawan kudin ruwan da ya ke dorawa kan basukan da ya ke bayar wa da akalla maki 700 a yau Juma'a, inda a yanzu kudin ruwan ya kai kashi 14.5 cikin 100.

Babban bankin Sri Lanka.
Babban bankin Sri Lanka. REUTERS - Dinuka Liyanawatte
Talla

Wannan mataki na zuwa ne a dai dai lokacin da 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa kan daruruwan daliban da ke zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki.

Matsalolin karancin abinci da man fetur da kuma wutar lantarki ne suka haifar da zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar ta Sri Lanka, inda dubban mutane ke kira ga shugaba Gotabaya Rajapaksa da ya yi murabus.

Yayin zanga-zangar ta baya-bayan nan dai dalibai sun yi yunkurin yin tattaki zuwa majalisar dokokin kasar a yau Juma’a.

A bangare guda kuwa, shugabannin mabiya addinin Buddah, wadanda galibinsu suka jagoranci yunkurin zaben Rajapaksa a watan Nuwamban 2019, sun fara shiga zanga-zangar adawa da shi a Colombo, babban birnin kasar ta Sri Lanka.

Masana tattalin arziki dai sun ce matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a kasar ita ce mafi muni da ta gani tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1948.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.