Ana zaben shugaban kasa a Cape Verde cikin rudanin tattalin arziki
Yan kasar Cape Verde sun fito rumfunan zabe a wannan Lahadi, don kada kada kuri'a a zaben shugaban kasa, cikin wani yanayi dake cike da muhawara kan makomar karamar kasar dake Yammacin Afirka da take fuskanatar matsin tattalin arziki sakamakon bullar annobar korona da ta hana yawon bude ido da kasar ke samun kudin shiga.
Wallafawa ranar:
Kafin barkewar cutar, kasar na samun kashi daya bisa hudu na kudin shigar ne ta hanyar baki daga kashen duniya dake yawon shakatawa.
'Yan takara 7 ke fafatawa a zaben, to sai dai tsoffin Franminista biyu ke kan gaba wato Carlos Veiga mai shekaru 72 da kuma Jose Maria Neves mai shekaru 60.
Ana sa ran samun sakamakon farko sa'o'i kadan bayan rufe rumfunan zabe da karfe 6:00 na yamma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu