Tarwatsewar bam ta jefa miliyoyin 'yan Afghanistan cikin duhu
Hukmomin Afghanistan sun ce miliyoyin mutane daga larduna 11 ne ke fuskantar rashin wutar lantarki a kasar a Asabar din nan, bayan aukuwar fashe fashe a wasu manyan turakun wutar lantarki a yammacin babban birnin kasar Kabul.
Wallafawa ranar:
Wannan rashin wutar lantarki na zuwa ne a daidai lokacin da ake daf da bukuwar salla karama ta Eid al- Fitir, wadda ke alamta karshen azumin watan Ramadan.
A daren Juma’a ne wasu suka dasa bama bamai a turakun lantarki 2, kuma suka tarwatse, lamarin da ya haddasa rashin wutar a babban birnin kasar da makwaftanta.
A yayin da hukumomi ke kokarin gudanar da gyara na wucin gadi do a samu wuta a daren Asabar dina nan, ‘yan sanda sun ce sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da dasa bama baman.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu