Isa ga babban shafi
Afghanistan - Pakistan

Adadin wadanda suka mutu a harin Pakistan kan Afghanistan ya karu zuwa 47

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da jiragen yakin Pakistan suka kai a lardin Khost da Kunar da ke gabashin Afganistan ya karu zuwa akalla 47, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Wani da ya jikkata sakamakon harin 'yan ta'adda a kasar Afganistan. 11/10/21
Wani da ya jikkata sakamakon harin 'yan ta'adda a kasar Afganistan. 11/10/21 AP - Mohammad Asif Khan
Talla

Daraktan watsa labaran yankin Khost Shabir Ahmad Osmani yace, Akalla fafaren hula 41 yawancinsu mata da kananan yara suka rasa rayukansu a harin na safiyar Asabar, yayin da 22 suka jikkata lokacin da sojojin Pakistan suka harba rokoki akan yankin da ke iyakarsu.

Wasu jami'ai biyu sun tabbatar da adadin wadanda suka mutu a Khost, yayin da wani jami'in Afghanistan ya ce a ranar Asabar an kashe mutane shida a lardin Kunar.

Tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe mulki a Afghanistan a shekarar da ta gabata, rikicin kan iyaka tsakanin kasashen da ke makwabtaka da kasar ya karu, inda Pakistan ke zargin cewa kungiyoyin 'yan ta'adda na kai mata hare-hare daga cikin kasar ta Afghanistan.

Sai dai kungiyar Taliban ta musanta zargin cewa tana baiwa mayaka masu ikirarin Jihadin da ke kaiwa Pakistan hare-hare mafaka, koda yake Taliban din ta bayyana fusata da wani shingen da Pakistan ke ginawa a kan iyakarsu mai tsawon kilomita dubu 2,700 da aka fi sani da layin Durand, wanda aka kafa a zamanin mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.