Isa ga babban shafi
Sri Lanka - Lanka

Fira ministan Sri lanka ya yi murabus

Fira ministan Sri lanka Mahinda Rajapaksa ya yi murabus bayan da gwamman  mutane  suka ji rauni a bayan da  magoya bayansa, dauke da sanduna suka afka wa masu zanga zanga.

Firaministan Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, wanda ya yi murabus.
Firaministan Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, wanda ya yi murabus. © AFP
Talla

Kasar ta sha fama da karancin wutar lantarki gami da na abinci da man fetur da magunguna  sakamakon fadawa matsalar tattalin arziki mafi muni tun bayan da ta samu ‘yancin kai, lamarin da ya janyo zanga zangar kin jinin gwamnati.

Kakakin Rajapaksa, Rohan Weliwita ya ce firaministan mai shekaru 76 ya aike da wasikar ajiye aiki zuwa ga kaninsa, shugaba  Gotabaya Rajapaksa, abin da ya share fagen kafa sabuwar gwamnati.

Tun da farko kafin tarzomar, babbar jam’iyyar adawa ta kasar   ta ce ba za ta shiga wata gwamnati da ke da iyalan gidan Rajapaksa a matsayin jagora ba.

Murabus da firaministan ya yi na nufin cewa an rushe majalisar dokokin kasar kenan, kuam za a gudanar da wani zabe.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa a Litinin din nan ne rikici mafi muni ya tashi a babban birnin kasar Colombo,  a lokacin da magoya bayan iyalan Rajapaksa suka afka wa masu zanga zanga.

‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi mai gishiri wajen tarwatsa masu zanga zangar, kuma suka ayyana dokar ta baci ba tare da bata lokaci ba a Colombo, wadda daga bisani suka fadada ta zuwa gaba daya sassan kasar mai yawan mutane miliyan 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.