Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa-Korona

Covid-19 ta yi sanadin mutuwar mutane 15 a Koriya ta Arewa

A ya Lahadi Koriya ta Arewa ta sanar da karin mutuwar mutane 15 cikin sa’o’I 24, bayan da a hukumance ta tabbatar da bullar cutar a karon farko a kasar, inda ta kakaba dokokin kulle.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un.
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un. AP
Talla

Bullar cutar wanda shugaba Kim Jung Un ya ce ta janyo tashin hankali, ya jefa kasar cikin hadarin fadawa cikin yanayi na annoba.

Koriya ta arewa ba ta da allurar rigakafin Covid-19 da kuma kayayyakin gwaji, ko ma magungunan dakile cutar.

A jiya Asabar ta sanar da mutuwar mutane 21 cikin sa’o’i 24 da suka harbu da cutar.

A ranar Juma’a kadai, sama da mutane miliyan 174,440 ne suka kamu da cutar, kuma dubu 81, 430 sun murmure, a yayin da 21 suka mutu, kamar yadda kamfanin dillancin labarn Koriya ta Arewar ta ruwaito.

A ranar Alhamis Koriya ta Arewar ta tabbatar da cewa an samu bullar Omicron, nau’in cutar Covid-19 mai saurin yaduwa a babban birnin kasar Pyonyang, inda shugaba Kim Jong Un ya yi umurnin dokar kulle  a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.