An tilastawa mata dake gabatar da shirye-shiryen talabijin rufe fuskokinsu
Mata 'Yan Jaridu dake gabatar da shirye shirye ta kafar Talabijin a kasar Afghansitan sun sha alawashin kalubalantar matakin da kungiyar Taliban ta dauka na tilasta musu rufe fuskokin su lokacin da suke gabatar da shirye shirye.
Wallafawa ranar:
Wannan umurnin ya sa mata da dama dake tashoshin talabijin na TOLONews da Ariana Television da Shamshad TV da kuma 1TV suka bi umurnin a jiya lahadi.
Shirin bijirewa matakin
Sonia Niazi, mai gabatar da shirye shirye a tashar TOLONews tace zasu ci gaba da bijirewa matakin wajen amfani da muryoyin su.
Mulkin Taliban
Tun bayan da kungiyar ta Taliban ta karbe mulki a shekarar da ta gabata, ta dauki tsauraran matakai kan kungiyoyin farar hula, inda da dama suka mayar da hankali wajen kwato 'yancin mata da 'yan mata wajen bin ka'idojin kungiyar ta Musulunci.
A farkon wannan watan, shugabar addinin Afganistan Hibatullah Akhundzada ya ba da sanarwar cewa mata su rufe gaba daya jikinsu a bainar jama'a, ciki har da fuskokinsu, wanda ya dace da burka na gargajiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu