Isa ga babban shafi
Amurka-Taliban

Amurka ta soke tattaunawa da Taliban saboda rufe makarantun mata

A jiya Juma’a  Amurka ta ce ta soke taron tattaunawa da ta shirya yi da kungiyar Taliban a birnin Doha na Qatar, bayan da kungiyar mai tsatsauran ra’ayin Islama ta rufe makarantun sakandiren mata a Afghanistan.

Joe Biden, shugan Amurka.
Joe Biden, shugan Amurka. AP - Patrick Semansky
Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurkar, Jalina Porter wadda ta sanar da wannan mataki, ta ce idan Taliban ba ta sauya shawararta ta rufe wadannan makarantun  wadda zai kasance illa ga al’ummarta ba, hakan zai shafi habakar tattalin arzikinta.

Kungiyar Taliban, wadda ta karbe mulki a watan Agustan shekarar da ta gabata, kuma ta zaku ta samu amincewar kasashen duniya, ta rufe makarantun matan ne ‘yan sa’o’i bayan da ta bude su.

Ma’aikatar harkokin wajen ta Amurka ta kuma bayyana goyon bayanta ga ilahirin ‘yaya mata na Afghanistan da iyalansu, wadanda suka dauki ilimi a matsayin hanyar cimma burukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.