Amurka ta gargadi China kan ayyukan sojinta a kusa da Taiwan
Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi Allah wadai da ayyukan soji da kasar China ke yi a kusa da Taiwan, da kuma yadda Beijing ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Asiya da tekun Pasific.
Wallafawa ranar:
Takaddama na kara tsami tsakanin Washington da Beijing kan Taiwan mai cin gashin kanta, wanda China ke kallo a matsayin yankinta, kuma ta sha alwashin kwace shi da karfin tuwo.
Beijing ta kai hare-hare da dama a yankin tsaron sararin samaniyar Taiwan a bana, kuma a ranar Juma'a, ministan tsaron kasar Wei Fenghe ya gargadi Austin cewa, kasar China a shirye take ta shiga yaki idan tsibirin ya ayyana 'yancin kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu