Girgizar kasa ta kashe karin mutane biyar a Afghanistan
Wani babban jami’in gwamnatin Afghanistan ya ce, kasar ba ta da wadatattun magungunan kulawa da wadanda suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,000 a makon da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Kalaman jami’in sun zo ne a yayin da, wata karamar girgizar kasar da ta afku a ranar Juma'a ta kashe karin mutane biyar.
A halin da ake ciki, mahukuntan Afghanistan sun kawo karshen laluben mutanen da suke yi a tsaunuka masu nisa dake kudu maso gabashin kasar domin neman wadanda suka tsira daga girgizar kasa mai karfin maki 6.1 da ta afku a safiyar ranar Laraba kusa da kan iyakar Pakistan.
Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar mutane 1,036, tare da jikkatar kimanin wasu 2000 a girgizar kasar ta ranar Laraba, kamar yadda Mohammad Nassim Haqqani, kakakin ma'aikatar kula da ayyukan jinkai ta Afghanistan, ya tabbatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu