Isa ga babban shafi

Kusan mutane dubu daya suka mutu sakamakon girgizar kasa a Afghanistan

Akalla mutane 920 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu, yayin da sama da 200 suka samu rauni sakamakon wata girgizar kasa mai karfin gaske da ta auku a Afghanistan a cikin daren da ya gabata.

Girgizar kasar ta yi rugu-rugu da gidajen al'umma a cewar rahotanni
Girgizar kasar ta yi rugu-rugu da gidajen al'umma a cewar rahotanni AFP/File
Talla

Ana fargabar adadin mamatan ya karu ganin irin girmar barnar da ibtila’in ya haifar a yankin Paktika da ke kusa da iyakar Pakistan.

Ma’aikatar Tunkarar Aukuwar Bala’o’i ta Afghanistan ta ce, an samu mafi asarar rayukan ne a Lardin na Paktika, inda anan kawai mutne 100 suka mutu.

Wasu hotuna da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda girgizar kasar ta yi rugu-rugu da gidajen al’umma.

Girgizar kasar dai na dauke da karfin maki 6.1 kamar yadda masana daga Amurka suka bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.