Isa ga babban shafi

Wani Kumbon China ya rikoto doron duniya daga sararin samaniya

Wani kunbo da China ta harba sararin samaniya ya rikito doron duniya, lamarin ya sanya hukumomin Amurka suka caccaki Beijing saboda rashin musayar bayanai game da gangarowar sa ganin  hadarin da yake tattare da shi.

Wani makamin da China ta harba sararin samaniya a ranar 24 ga watan Yuli, 2022.
Wani makamin da China ta harba sararin samaniya a ranar 24 ga watan Yuli, 2022. AP - Li Gang
Talla

A cikin wata sanarwa da hukumar kula da sararin samaniya China ta fitar a shafinta na WeChat, ta ce ya fado ne a tekun Sulu mai tazarar kilomita 57 daga gabar gabashin tsibirin Palawan na Philippines.

Malaysia

Hukumar kula da sararin samaniyar Malaysia, ta ce taga wasu barabuzai naci da wuta kafin faduwar su a tekun Sulu da ke arewa maso Gabashin tsuburin Borneo.

Amurka

Shugaban hukumar kulada sararin samaniyar Amurka Bill Nelson ya soki Beijing a shafin sa na twitter, inda ya ce rashin sanar da batun rikitowar kunbon na China bai kamata ba domin yana tattare da hatsarin gaske.

Tashar sararin samaniya ta Tiangong na daya daga cikin kudurorin da China ke son cimmawa a sararin samaniya, wanda ya sanya ta harba mutummutumi a duniyar Mars da kuma duniyar wata, lamarin da ya sanya China zama kasa ta uku da ta tura dan Adam a sararin samaniya.

Kaddamarwa

Lokacin da China ta kaddamar da tashar Tiangong ta farko a watan Afrilun 2021, an sami irin wannan hatsarin.

A shekarar 2020, barabuzan wani kunbon China sun fado a wani kauye a Ivory Coast, wanda yayi sanadiyar asarar dukiya mai yawa amma ba’a samu asarar rayuka ba.

Kasar China ta zuba biliyoyin daloli a harkar binciken sararin samaniya, a kokarin ta na ganin ta samu karfin fada a ji a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.