Isa ga babban shafi

ASEAN ta gargadi Myanmar kan aiwatar da hukuncin kisa kan fursinoni

Cambodia da ke shugabancin kungiyar ASEAN mai kunshe da hadakar kasashe 10 na yankin kudu maso gabashin Asiya, ta gargadi Myanmar game da sake aiwatar da hukuncin kisa kan fursunonin da ta ke tsare da su, gargadin da ke zuwa bayan kasar ta kashe wasu mutum 2 ta hanyar rataya.

Taron kungiyar ASEAN da ya gudana a Cambodia.
Taron kungiyar ASEAN da ya gudana a Cambodia. AP - Susan Walsh
Talla

Yayin taron ministocin wajen kungiyar ta ASEAN a birnin Phnom Penh na Cambodia sun mayar da hankali kan halin da ake ciki a Myanmar kasar da Soji ke jagoranci tun bayan hambarar da gwamnatin Aung San suu Kyi a bara.

A watan jiya ne Sojin da ke shugabancin kasar ta Myanmar suka aiwatar da hukuncin kisan kan mutane 4 ciki har da wasu fitattun masu fafutukar tabbatar da demokradiyya biyu.

Matakin aiwatar da hukuncin kisan dai ya ja hankalin kasashen Duniya da masu rajin tabbatuwar demokradiyya musamma  Amurka da ke kan gaba wajen caccakar salon kamun ludayin Sojojin da ke mulkin kasar.

Cikin watan Aprilun da ya gabata ne dai aka cimma yarjejeniyar kawo karshen zubda jini tare da sasantawa tsakanin Sojin da bangarorin adawa.

Firaministan Cambodia da ya jagoranci taron na ASEAN Hun Sen ya ce kungiyar ta fusata da matakin sojin wanda ta bayyana da tsantsar take hakkin dan adam.

Taron dai ya gudana ba tare da wakilcin Myanmar ba, sai dai kungiyar ta ce dole ne Sojin su sauya hukuncin da suka yankewa da dama daga cikin fursinonin da ke tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.