Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane sama da 800 a Pakistan

Ma'aikatar kula da yanayi a Pakistan ta ce mamakon ruwan sama a daminar bana, ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa a sassan kasar, wadda kuma daga watan Yuni zuwa yanzu ta kashe mutane sama da 800 yayinda yankuna da dama ke cikin matsanancin bukatar agaji.

Wani yanki da ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan.
Wani yanki da ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan. ASSOCIATED PRESS - Khalid Tanveer
Talla

Ministan kula da yanayi na Pakistan Sherry Rehman ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya ya ci gaba da mamaye wasu sassa na Pakistan a larabar nan, inda hukumomi suka bayar da rahoton mutuwar mutane da dama ciki har da yara tara a kasa da sa'o'i 24 da suka gabata.

Wata mata mai suna Khanzadi ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, an kwashe wata guda ana ruwan sama, babu kakkautawa a yankin Balochistan.

A cewarta kakkarfan ruwan ya rushe gidan da su ke baya ga yin awon gaba da akuya daya tilo da ta mallaka, wanda ya sanya su kwana a titi cikin halin matsananciyar yunwa.

Ministan yanayin Sherry Rehman ta ce hukumomi za su kaddamar da neman taimako daga kasashen duniya da zarar an kammala tantance abubuwan da suka faru don agazawa mutanen da ambaliyar ta shafa.

Kididdigar da wata kungiya mai sanya ido akan harkokin sauyin yanayi, ta bayyana cewa Pakistan na matsayi ta takwas a cikin jerin kasashen da ake ganin sun fi fuskantar matsanancin yanayi sakamakon sauyin yanayi.

A cikin wata sanarwa da hukumar da ke kula da annoba ta kasar ta fitar ta ce kusan gidaje dubu 125 ne ambaliyar ta yi awon gaba da su yayinda ta lalata wasu gidajen na daban akalla dubu 288.

Hukumomin Pakistan sun bayyana yadda ambaliyar zuwa yanzu ta kashe kimanin dabbobi dubu 700,000 a yankunan Sindh da Balochistan, sannan ta lalata kusan kadadar noma miliyan biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.