Isa ga babban shafi

Guterres ya roki kasashe su taimawa Pakistan gabanin ziyararsa a makon gobe

Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce zai kai ziyara cikin makon gobe a kasar Pakistan, domin nuna alhini dangane da irin barna da kuma asarar rayukan da aka samu sanadiyyar mummunar ambaliyar ruwan da kasar ke gani.

Zuwa yanzu ruwa ya shanye kashi 3 bisa dari na fadin kasar yayinda mutane fiye da dubu guda suka mutu, baya ga miliyoyi da suka rasa matsugunansu.
Zuwa yanzu ruwa ya shanye kashi 3 bisa dari na fadin kasar yayinda mutane fiye da dubu guda suka mutu, baya ga miliyoyi da suka rasa matsugunansu. © AP - Zahid Hussain
Talla

Guterres wanda ya mika bukatar tattara tallafin da ya kai dala miliyan 160 don taimakawa Pakistan, a wani sako da ya fitar da kansa, ya bukaci kasashen duniya su taimaka wa Pakistan sakamakon wannan yanayi da ta samu kanta.

zuwa yanzu miliyoyin mutane ne suka rasa matsugunansu yayinda gwamnati ka kafa sansanoni don baiwa mutane mafaka.

Mai magana da yawun sakataren na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ruwaito Guterres na cewa makarantu da muhimman cibiyoyi da kuma abinci sun lalace, haka zalika ambaliyar ta mamaye da kuma lalata  sauran muhimman abubuwa na more rayuwa a sassan kasar.

Guterres yakuma shawarci hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakan gaggawa domin taimaka wa jama’ar Pakistan, domin kuwa yanzu haka akwai milyoyin mutane da ke rayuwa ba cikin muhallansu ba.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar wanda ya bayyana matukar kaduwa da ganin halin da al'ummar Pakistan ke ciki ya yabawa matakan da gwamnatin kasar ke dauka wajen taimakon wadanda ambaliyar ta shafa.

Guterres ya mika kokon bara ga manyan kassahe da sauran manyan kungiyoyi don ganin sun tallafawa kasar ta Pakistan.

Fiye da mutum dubu guda suka mutu a ambaliyar yayinda ruwa ya shanye kashi 3 na fadin kasar ta yankin Asiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.