Isa ga babban shafi

Mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan sun haura 1000

A yayin da adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan ya haura 1000, ana fargabar samun ambaliyar ruwa a lardin Sindh dake arewacin Kasar sakamakon cikar da kogunan yankin suka yi.

Mutane da dama ne suka bace sakamakon ambaliyar ruwan
Mutane da dama ne suka bace sakamakon ambaliyar ruwan AP - Zahid Hussain
Talla

Tuni dai Babban kogin Indus da ya ratsa yanki na biyu mafi yawan alumma a Pakistan, ya cika makil da tsaunukan da ruwa ya kwashe, bayaga kananan rafi dake wucewa ta cikin shi.

Hukumomin Kasar sun yi gargadi a kan cewa nan da kwanaki masu zuwa da yiwuwa a fuskanci ambaliya a lardin Sindh, karin bala’i a kan wanda miliyoyin alummar Kasar ke ciki a halin yanzu.

A jiya lahadi ne Hukumar kula da bala’o’I ta Pakistan NDMA ta ce akalla mutane 1033 suka mutu sakamakon ambaliyar, bayan samun karin mutane 119 kasa da sa’oi 24 kafin nan.

Tuni dai gwamnatin Pakistan ta sake yin kira ga dubban mazauna lardin Sindh dake arewacin Kasar su gaggauta ficewa daga yankunansu dan tsira da rayukansu, la’akari da yadda ruwa ke cigaba da taruwa.

Kawo yanzu dai ambaliyar wannan shekara da ta samo asali sakamakon kakkarfar ruwan sama da ake ta yi babu kakkautawa ya shafi sama da mutane miliyan 33 galibi mazauna karkara, bayaga yin awon gaba da tarin gidaje da kuma dukiyoyi, ya kuma lalata gonakin da da fadinsu ya kai kadada miliyan 2 a sassan Kasar.

Rabon da ayi Mumunar ambaliyar makamancin wannan, tun a shekarar 2010, wanda ake kallo a matsayi mafi muni da Pakistan ta taba fuskanta sakamakon kashe mutane 2000 tare da mamaye kusan kaso 5 na fadin Kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.