Isa ga babban shafi

Ma'aikatar shari'ar Iran ta nesanta kisan Mahsa da zanga-zangar da kasar ke gani

Ma’aikatar shari’ar Iran ta nesanta alaka tsakanin mutuwar matashiya Mahsa Amini da kuma zanga-zangar da kasar ke gani inda nanata cewa sam boren da ke faruwa a sassan kasar ba shi da alaka da mutuwar, wadda ake dangantawa ga jami'an 'yan sandan tabbatar da da'a.

Masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini a Iran.
Masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini a Iran. AP - Aurelien Morissard
Talla

Tarzoma ta barke a sassan Iran ne tun bayan da Mahsa Amini mai shekaru 22 ta rasu a ranar 16 ga watan Satumba bayan 'yan sanda tabbatar da da'a sun kama ta a birnin Tehran bisa laifin kin sanya hijabi.

Zuwa yanzu fiye da mutane 130 suka mutu a zanga-zangar yayinda aka kame daruruwan masu tarzoma wadanda gwamnati ta zarga da haddasa tashin tashina a kan titunan kasar.

Ma'aikatar shari'ar Iran bayan dogon bincike kan zarge-zargen cewa jami'an tsaron ne suka kashe Mahsa 'yar kabilar kurdawa sun bayyana cewa sam babu wasu hujjoji ko alamu da ke nuna jami'an ne suka kashe Matashiya.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya ruwaito wani jami'in ma’aikatar shari'a Mohammad Shahriari na cewa Gwaje-gwajen kwararru da aka yiwa gawar matashiyar sun tabbatar da karaya a bangarorin jikinta da dama wanda ke nuni da cewa an jefo ta ne daga wani wuri mai tsawo amma babu alamar harbi a jikinta.

Iyayen matashiyar dai na ganin akwai yiwuwar jami'an sun lakada mata duka ne, wanda ya yi musabbabin mutuwarta.

Tuni dai kisan ya janyowa Iran karin takunkumai daga kasashen Duniya yayin da masu zanga-zangar ke samun goyon baya daga sassa daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.