Isa ga babban shafi

WHO za ta taimakawa China don kawar da cutar covid-19 da ke ci gaba da yaduwa

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci mahukuntan kasar China da su kaddamar da gagarumin aikin yi wa al’umma rigakafi musamman a yankunan da ke fama da cutar covid19.

Wasu bayanai na nuni da cewa ana ci gaba da samun karuwar masu harbuwa da cutar Covid-19 a sassan China.
Wasu bayanai na nuni da cewa ana ci gaba da samun karuwar masu harbuwa da cutar Covid-19 a sassan China. AFP - -
Talla

Shugaban hukumar ta lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus, wanda ke wannan batu bayan rahotannin tsanantar cutar ta covid-19 a wasu sassa na China ya ce hukumarsa a shriye ta ke domin taimaka wa China ta yaki wannan cuta.

A cewar Tedros Adhanom WHO ta damu matuka a game da yanayin kiwon lafiya a China, musamman yadda wannan annoba ke dada kamari.

Shugaban na hukumar lafiya ya ce don tantance hakikanin abinda ke faruwa,  WHO na bukatar cikakkun bayanai musamman daga asibitoci da sauran hukumomin kiwon lafiya.

Tedros Adhanom wanda ya nuna cikakken goyon baya ga salon da China ke dauka don shawo kan wannan annoba ciki har da shirin fara yi wa jama’a allurar rigakafi a yankunan da annobar ta fi yi wa barazana, ya ce za su ci gaba da taimaka wa kasar don jinyar wadanda suka harbu da kwayar cutar da kuma kare bangaren kiwon lafiya na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.