Isa ga babban shafi

WHO ta bukaci China da ta kara inganta shirin rigakafin Covid19

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci mahukuntan kasar China da su kaddamar da gagarumin aikin yi wa al’umma rigakafi musamman a yankunan da ke fama da cutar covid19.

Wani jami'in lafiya kenan, lokacin da yake daukar samfuri domin gwajin COVID-19 a Wuhan da ke tsakiyar kasar China
Wani jami'in lafiya kenan, lokacin da yake daukar samfuri domin gwajin COVID-19 a Wuhan da ke tsakiyar kasar China AP
Talla

Shugaban hukumar ta lafiya Tedros Adnom Gebreyesus, ya ce hukumarsa a shriye take domin taimaka wa China ta yaki wannan cuta.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta damu matuka a game da yanayin kiwon lafiya a China, musamman yadda wannan annoba ke dada kamari.

Domin tantance hakikanin abinda ke faruwa, hukumar WHO na bukatar cikakkun bayanai musamman daga asibitoci da sauran hukumomin kiwon lafiya.

"Muna goyon bayan irin matakan da China ke dauka don shawo kan wannan annoba ciki har da shirin fara yi wa jama’a allurar rigakafi a yankunan da annobar ta fi yi wa barazana," in ji Gebreyesus.

"Za mu ci gaba da taimaka wa kasar don jinyar wadanda suka harbu da kwayar cutar da kuma kare bangaren kiwon lafiya na kasar," a cewar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.