Isa ga babban shafi

China za ta kawo karshen killace bakin da suka shigo daga ketare

Gwamnatin China za ta kawo karshen kebance matafiya saboda cutar corona daga ranar 8 ga Janairu, matakin da ke nufin kasar za ta bude kanta ga baki daga sauran kasashe, bayan shafe shekaru uku ta na rufe iyakokinta.

Sashen killace masu cutar Corona a China.
Sashen killace masu cutar Corona a China. VIA REUTERS - CHINA DAILY
Talla

Matakin daina killace baki matafiya da zarar sun isa kasar ta Sin din dai zai shafi ma’aikata ne da dalibai da kuma masu ziyartar iyalai da sauran dangogi.

Sai dai shirin na China ya zo ne yayin da kasar ke fuskantar sake yaduwar annobar Korona inda asibitoci da dama suka sun cika, yayin da kuma ake samun mutuwar tsofaffi.

Jami’an Lafiya sun ba da rahoton cewa a kan samu mutane akalla dubu 4 a kowace rana da ke kamuwa da cutar a makon da ya gabata sai dai kalilan daga cikinsu ne ke mutuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.