Isa ga babban shafi

Koriya ta Kudu za ta biya diyya ga wadanda suka yi aikin dole lokacin yakin Japan

Koriya ta Kudu ta sanar da shirye-shiryen biyan diyya ga wadanda aka sanya aikin dole a lokacin yakin Japan, a kokarin da take na yaukaka dangantaka da Japan, don taka wa makwafaciyarta, Koriya ta Arewa birki.

Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol, 1 ga watan Maris, 2023.
Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol, 1 ga watan Maris, 2023. via REUTERS - POOL
Talla

Kimanin ‘yan Koriya dubu dari 7 da 80 ne Japan ta dauke su aikin dole a tsawon shekaru 35 da ta yi tana mamayar kasarsu, idan aka debe mata da dakarun Japan din suka yi lalata da su da karfin tuwo.

Ministan Harkokin Wajen Koriya ta Kudu, Park Jin ne ya bayyana wadannan shirye-shirye, inda biyan diyya ga iyalan wadannan mutane, yana mai bayyana fatan hadin kai daga Japan.

Tun da farko kafafen yada labaran Japan sun ruwaito cewa kamfanonin kasar za su bayar da gudummawar kudi, a yayin da ake sa ran kasar ta nemi afuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.