Isa ga babban shafi
Koriya ta Kudu- Rasha

Koriya ta Kudu ta harbo jirgin Rasha a samaniyarta

Kasar Koriya ta Kudu ta ce, ta yi harbin gargadi kan jirgin leken asiri mallakin Rasha da ya ratsa sararirin samaniyarta a wannan Talata.

Samfurin jirgin yakin da Koriya ta Kudu ta yi amfani da shi wajen harbin jirgin leken asirin Rasha
Samfurin jirgin yakin da Koriya ta Kudu ta yi amfani da shi wajen harbin jirgin leken asirin Rasha AFP/JACK GUEZ
Talla

Hukumomin kasar sun ce, sau biyu jirgin ke karya dokokin ratsa samaniyar a tsibirran Dokdo/Takeshima da gwamnatin Seoul ta mamaye duk da ikirarin kasar Jordan da ita ma ke cewa, mallakinta ne.

Ma’aikatar Tsaron Koriya ta Kudu ta ce, cikin gaggawa ta yi amfani da jiragen yaki domin mayar da martani, inda ta harba bindiga mai aman wuta samfurin 360.

Kasar Rasha ta musanta keta sararin samaniyar Koriya ta Kudu, tana mai cewa, wasu jiragen yakinta guda biyu ne suka gudanar da wani shiryen-shiryen atisaye akan tekun da ba ya karkashin mallakar wata kasa, yayinda kuma ta musanta harbin gargadin daga Koriya ta Kudu.

A karon farko kenan da ake samun irin wannan tankiya tsakanin Koriya ta Kudu da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.