Isa ga babban shafi

Akalla mutane 22 suka mutu bayan kifewar kwale-kwalensu a Indiya

Akalla mutane 22 ne suka mutu a kasar India bayan da wani kwale-kwalen yawon bude ido mai hawa biyu ya kife a jihar Kerala da ke kudancin kasar.

Akalla mutane 22 ne suka mutu a kasar India bayan da wani kwale-kwalen yawon bude ido mai hawa biyu ya kife a jihar Kerala da ke kudancin kasar.7/05/23.
Akalla mutane 22 ne suka mutu a kasar India bayan da wani kwale-kwalen yawon bude ido mai hawa biyu ya kife a jihar Kerala da ke kudancin kasar.7/05/23. AP - P.P. Afthab
Talla

Jami’ai a kasar suka ce lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi a Tanur, wani gari da ke gabar teku a gundumar Malappuram ta Kerala, kuma ana ci gaba da ayyukan ceto.

Mutane da dama ne suka yi ta neman wadanda suka tsira a ciki da wajen jirgin da ya rutsa da su cikin dare, wanda wani bangare ya nutse. Wasu sun yi amfani da igiya wajen dakatar da jirgin yayin da wasu ke cikin ruwa, suna lalube.

Akalla mutane 22 ne suka mutu a kasar India bayan da wani kwale-kwalen yawon bude ido mai hawa biyu ya kife a jihar Kerala da ke kudancin kasar.7/05/23
Akalla mutane 22 ne suka mutu a kasar India bayan da wani kwale-kwalen yawon bude ido mai hawa biyu ya kife a jihar Kerala da ke kudancin kasar.7/05/23 AP - P.P. Afthab

Jami’in ya kara da cewa akwai mutane kusan 30 a cikin jirgin lokacin da ya tashi.

Iyalan gida daya sun mutu

Jaridar Onmanorama ta kasar ta ruwaito cewa mutane 11 daga iyali daya da suka hada da yara uku sun mutu a hatsarin.

Ministan wasanni da kamun kifi na jihar V. Abdurahiman wanda ya taimaka wajen daidaita ayyukan ceto ya ce yawancin wadanda abin ya shafa yara ne dake hutun makaranta.

Abdurahiman ya ce an kai mutane hudu asibiti cikin mawuyacin hali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Press Trust ya ruwaito.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.