Isa ga babban shafi

Rikicin kabilanci ya kashe mutane 40 a jihar Manipur ta arewacin India

Rahotanni daga India sun ce kimanin mutane 40 da ake zargin ‘yan tsagera ne suka mutu tare da wasu ‘yan sanda 2 a jihar Manipur da ke arewa maso gabashin kasar, sakamakon barkewar wani sabon rikicin kabilanci. 

Wani yanki da rikicin kabilancin ya shafa.
Wani yanki da rikicin kabilancin ya shafa. © AFP
Talla

Jihar Manipur ta shiga halin kaka-ni-ka-yi bayan da barkewar rikicin kabilanci a farkon wannan watan ya yi sanadin mutuwar mutane 70, kana ya daidaita dubun dubata. 

Wani babban jami’i a jihar ta Manipur, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce babban ministan jihar N. Biren Singh ya shaidaa wa manema labarai a  safiyar Lahadin nan cewa jami’an tsaro sun kashe kimannin ‘yan tsagera masu dauke da makamai a cikin kwanaki biyu da suka gabata. 

Tun da farko a ranar Lahadi, kafafen yada labaran India sun ruwaito Singh yana cewa ‘yan tsageran da ke aikata ta’addanci suna amfani ne da bindigogi kirar M-16 da AK-47 a kan fararen hula, kuma suna tada duk wani kauyen da suka shiga. 

Jihar Manipur, wanda take a tsakanin kasashen Bangladesh, China da Myanmar ta dade cikin yanayi na zaman tankiya a tsakanin kabilu dabam-dabam da ke cikinta. 

A farkon watan Mayu, mummunan rikicin kabilanci ya auku a jihar Manipur a tsakanin kabilar Meitei masu rinjaye, wadanda akasarinsu mabiya addinin Hindu ne, da kabilar Kuki, wadanda mafi yawan su kiristoci ne, inda aka samu asarar dimbim rayuka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.