Isa ga babban shafi

Tsananin zafi ya kashe kusan mutane 100 a kasar India

Mutane da dama ne suka mutu a wasu sassan kasar India a cikin ’yan kwanaki,  a yayin da mahukunta ke kokarin tantace ko tsananin zafin da ake fuskanta a kasar ne ya kawo wannan asarar rayuka. 

Wani ma'ikaci dake kare kansa daga tsananin zafin rana a kasar India.
Wani ma'ikaci dake kare kansa daga tsananin zafin rana a kasar India. AP - Rajesh Kumar Singh
Talla

 

Jimillar mutane 96 ne suka mutu a arewacin jihar Uttar Pradesh da gabashin Bihar, a yayin da hukumar kula da yanayi ta kasar ke gargadin cewa za a fuskanaci tsananin zafi a sauran yankuna arewa maso gabashin kasar. 

Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar India ta sanar da cewa yanayin zafi ya tashi zuwa digiri 42 zuwa 45 a ma’aunin Celsius a jihohi 5 a karshen makon da ya gabata, tana mai shawartar mutane su kasancea cikin gidajensu a yayin da yanayin ke kara zafafa. 

Gwamnatin kasar tace tana gudanar da bincike  a game ca musabbabin mutuwar mutane a cikin kwanaki 3 na makon da ya gabata a gundumar Ballia ta jihar Uttar Pradesh, mai nisan kilomita 970 daga kudu maso gabashin birnin New Delhi. 

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan da kantoman gundumar ta Ballia Ravindra Kumar ya bayyan  a  shakkun ko mace macen da suka auku sakamako ne na yanayinn tsanannin zafi da ake fuskanta. 

A wasu sassa, wannan lamari daai ya fi shafar mutane ne ne masu yawan shekaru. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.