Isa ga babban shafi
India-Guguwa

Guguwar Tauktae na cigaba da tafka barna a India

Gwamnatin India tace akalla mutane 33 suka mutu, yayin da wasu sama da 90 suka bata sakamakon mahaukaciyar guguwa mai dauke da ruwan sama ta afkawa kasar India.

Yadda guguwar Tauktae ta hautsina gabar ruwan teku da yayi iyaka da birnin Mumbai a India. 17/5/2021.
Yadda guguwar Tauktae ta hautsina gabar ruwan teku da yayi iyaka da birnin Mumbai a India. 17/5/2021. REUTERS - NIHARIKA KULKARNI
Talla

Rahotanni sun ce daruruwan mutane yanzu haka suna zama cikin duhu sakamakon katsewar wutar lantarki bayan da guguwar ta afkawa Gujurat inda tayi mummunar ta’adi.

Hukumar kula da yanayi tace guguwar mai tafiyar kilomita 130 cikin sa’a guda ta karya daruruwan itatuwa da turakun lantarki da kware rufin gidaje.

Jami’ai sun ce guguwar da aka yiwa lakabi da Tauktae na tsala gudun kilomita 130 a sa’a 1 yayinda ta haddasa murdawar igiyar ruwan da tsawonta ya kai mita 8 a tsaye, wadda ta dulmiyar da wani jirgin ruwan safarar man fetur da masu sikin hakosa a gabar ruwan birnin Mumbai, abinda ya sanya batan mutane 96 daga cikin 273 daga cikin jirgin.

Ma’aikatar tsaron India ta ce zuwa yanzu gidaje fiye da dubu 16 da 500 guguwar ta Tauktae ta rusa, tare da tuge bishiyoyi kimanin dubu 40, sai kuma kauyuka akalla dubu 2 da 400 da suka rasa hasken lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.