An kwashe mutane fiye da dubu 100 saboda ambaliyar ruwa a Pakistan
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta kasar Pakistan ta sanar da cewa, kimanin mutane 100,000 ne aka kwashe daga kauyukan da ambaliyar ruwa ta mamaye a lardin Punjab na kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kauyuka da dama da dubban kadada na gonakin noma a lardin tsakiyar kasar sun kasance a cikin ruwa lokacin da kogin Sutlej ya balle a ranar Lahadi.
Shugaban gwamnatin Punjab, Mohsin Naqvi, ya ce ruwan sama ya sanya hukumomi a India sakin ruwa mai yawa a cikin kogin Sutlej, wanda ya haifar da ambaliya a gefen iyakar Pakistan.
" Ruwan ya zo ne kwanaki biyu da suka gabata kuma dukkanin gidajenmu sun nutse," in ji Nagvi wani mazaunin yakin da ke shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP abin da ya faru.
Kasar da ke Kudancin Asiya, na samun kashi 70-80 cikin 100 na ruwan sama a tsakanin watan Yuni da Satumban kowace shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu