Isa ga babban shafi

Mutane 18 sun kone kurmus sakamakon hatsarin mota a Pakistan

Akalla mutane 18 ne suka mutu bayan da wata motar safa ta fadi kuma ta kama wuta a lardin Punjab da ke gabashin Pakistan a ranar Lahadi, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Masu aikin ceto kenan yayin wani daukin gaggawa a Ghotki na kasar Pakistan, bayan wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya auku a watan Yunin 2021.
Masu aikin ceto kenan yayin wani daukin gaggawa a Ghotki na kasar Pakistan, bayan wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya auku a watan Yunin 2021. REUTERS - STINGER
Talla

Motar bas din ta yi karo da wata motar da sanyin safiya yayin da take dauke da fasinjoji 33 daga birnin Karachi mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin kasar zuwa Islamabad babban birnin kasar.

"Bas din ta yi karo da wata karamar mota makare da kananan tankokin mai guda uku da misalin karfe 4:30 na safe," in ji Fahad Ahmad, shugaban 'yan sanda na gundumar Hafizabad ta Punjab.

Ya ce an kai wasu mutane 16 da suka samu munanan raunuka asibiti.

Ana yawan samun munanan hadurran motoci a Pakistan, inda ba kasafai ake bin ka'idojin zirga-zirga ba, kuma hanyoyin da ke yankunan karkara da dama ba su da kyau.

Fiye da mutane 40 ne suka mutu e a cikin watan Janairu bayan da wata motar safa ta fada cikin wani rafi ta kuma kama da wuta a lardin Balochistan da ke kudancin Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.