Isa ga babban shafi

Kasashe sun fara aikewa Pakistan agaji bayan ambaliya ta kashe mutane dubu 1 da 300

Jirage makare da kayakin agaji sun fara isa Pakistan yau juma’a don tallafawa miliyoyin ‘yan kasar da ambaliyar ruwa ta shafa dai dai lokacin wadanda ambaliyar ta kashe ke haura mutum dubu 1 da dari biyu, inda ake fargabar yiwuwar barkewar cutuka masu alaka da tsaftar muhalli musamman la’akari da yadda miliyoyin ‘yan kasar yanzu haka ke rayuwa akan tituna.

Zuwa yanzu Iyalai miliyan 3 da rabi ambaliyar ta shafa.
Zuwa yanzu Iyalai miliyan 3 da rabi ambaliyar ta shafa. AP - Zahid Hussain
Talla

Wannan dai shi ne jirgi na 9 da Hadaddiyar daular larabawa ta aikewa Pakistan tun bayan tsanantar ambaliyar yayinda jirgin farko na daban daga Uzbekistan ya sauka a Islamadad da safiyar yau juma’a dauke da kayakin agaji.

Wasu bayanai sun ce tuni kayakin agajin da hadaddiyar daular larabawa ta aikewa Pakistan ya isa ga mutane sama da miliyan 3 da ambaliyar ta shafa a sassan kasar.

Masana da dama dai na ci gaba da dora alhakin ita wannan ambaliya kan sauyi ko kuma dumamar yanayi da Duniya ke fuskanta, ciki har da sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres wanda cikin makon nan ya yi kira da a kawo karshen tafiyar hawainiya a kokarin samar da dokokin yaki da dumamar yanayi.

Wata sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta fitar, ta ce jiragen sun bayar da agajin kayakin abinci da magunguna da tantin da wadanda suka rasa matsugunansu za su yi amfani da shi.

A asabar mai zuwa ne Firaminista Shahbaz Sharif zai ziyarci yankin da ambaliyar ta faru bayan da ya dakatar da ziyarar da ya tsara kaiwa hadaddiyar daular larabawa.

Zuwa yanzu Pakistan ta karbi agaji daga kasashen China da Saudi Arabia da Qatar da Turkiya da Uzbekistan da kuma hadaddiyar daular larabawa akan gaba.

Haka zalika Amurka ta yi alkawarin taimakon kasar da kayakin agajin dala miliyan 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.