Ba zamu daina kashe makudan kudade don farfado da League din Saudiyya ba-Bin Salman
A nan kuma Yarima mai jiran gadon Saudiyya Muhammad Bin Salman ya mayar da zazzafan martani ga masu sukar kasar, wajen kashe zunzurutun kudade a harkokin wasanni dama sayen ‘yan wasa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kamar dai yadda aka sani, a baya-bayan nan Saudi Arabiya na zuba kudade na ban mamaki wajen farfado da gasar League din kasar tare da siyan zaratan ‘yan wasa kan kudade masu tarin yawa.
To sai dai tuni kungiyoyi musamman na kare hakkin dan adam suka fara suka yariman, yayin da suke ganin wannan sam barnar kudi ne a kasar da hakkin dan adam bashi da wata kima.
Yayin da ya ke zantawa da gidan talabijin na Fox, Yarima Salman, ya ce idan kashe tsabar kudi wajen farfado da gasar League din kasar zai daga darajar tattalin arzikin Saudiyya da kaso daya tak, to ba shakka zai ci gaba da haka.
Yariman yace duk ma abinda masu suka zasu kira yunkurin nasa su kira, amma matukar hakan zai tasiri ga tattalin arzikin Saudiyya, to kuwa babu abinda zai dakatar da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu