Isa ga babban shafi

Gobara ta kashe mutane sama da 100 a kasar Iraqi

Wata gobara da ta  tashi a yankin Al-Hamdaniyya na kasar Iraqi ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 115, yayin da wasu 200 ke kwance a asibiti sakamakon kuna ko kuma rashin numfashi sanadin turnukewar hayaki.

Har yanzu babu tabbas kan alkalman mutanen da gobarar ta kashe
Har yanzu babu tabbas kan alkalman mutanen da gobarar ta kashe REUTERS - KHALID AL-MOUSILY
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa wutar ta tashi ne a wani babban dakin taro, inda ake gudanar da bikin aure.

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Iraqi Shafaq,  ya ruwaito wutar ta tashi ne lokacin da ake tsaka da shagalin bikin auren cikin daren jiya Talata.

A nata bangaren, ma’aikatar lafiyar kasar ta bakin kakakinta Saif Al-Badr ta shaidawa manema labarai cewa gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen ci gaba a bincike don gano wasu gawarwakin, inda kuma ake cigaba da kulawa da wadanda suka jikkata.

A nasa bangaren shugaban hukumar farin kaya na kasar Brigediya Janar Jawdat Abdel Rahman, ya ce wutar ta tashi ne a sakamakon ganganci da kuma sakacin da aka yi da wutar da aka yi amfani da ita wajen kawata dakin taron.

Tun farko dai an kawata dakin taron ne da wuta mai ci bisa al’adun gargajiyar jama’ar garin, yayin da masu wasan wuta suka fara nuna bajintar su, nan ne kuma wutar ta kwace inda gobara mai muni ta tashi, wanda ta shafi mata da kananan yara.

Bayanai sun nuna cewa wutar ta yi tsananin da ta rusa dakin taron, wanda ya fada kan mutanen da wuta ta kama jikinsu.

Wani bangare na dakin taron da gobara ta tashi a Iraqi da ya rushe.
Wani bangare na dakin taron da gobara ta tashi a Iraqi da ya rushe. REUTERS - KHALID AL-MOUSILY

Ofishin Fara ministan kasar Muhammad Shiaa Al-Sudani ya ce a binciken farko-farko da aka gudanar an gano cewa ba a ajiye kayayyakin bada agajin gaggawa da na kashe gobara matsayin ko ta kwana a wajen ba, lamarin da ya baiwa gobarar damar yin muni kafin zuwa jami’an kashe gobara.

Tuni dai ofishin ministan cikin gida ya bada umarnin fara rarraba marasa lafiya zuwa asibitoci daban-daban don kulawa da su cikin gaggawa.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan ko Amarya da Ango na cikin wadanda suka rasa ransu ko kuma suka jikkata sanadin gobarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.